Badaru ya ga laifin Lamido kan halin da makarantun Jigawa ke ciki

Badaru ya ga laifin Lamido kan halin da makarantun Jigawa ke ciki

- Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar ya zargi tsohon gwamna Sule Lamido da sanya makarantun jihar Jigawa cikin halin da suka shiga

- Ya bayyana cewa bidiyon da yayi fice dake nuni ga halin da makarantun jihar Jigawa ke ciki ya kasance tabbaci na yadda hukumar ilimi ta tagayyara a karkashin tsohon gwamna Lamido

- Badaru yace gwamnatinsa na kokari don ganin ta magance matsalar

Gwamnan jihar Jigawa, Mohammed Badaru Abubakar, yace bidiyo da aka yada ta yanar gizo wanda ke nuni ga mumunar yanayi da makarantun firamare da sakondare ke ciki a jiharsa ya kasance shaidar yanda fannin ilimi ta sha wuya a shekaru da dama da suka gabata a gwamnatin tsohon gwamna Sule Lamido.

Badaru ya fadi hakane yayinda yake kaddamar da ofishin yanki na dan majalisan wakilai, mai wakiltan yankin Birniwa, Kirikasamma, Abubakar Fulata a Kirikasamma.

Yayi watsi da dangantakar bidiyon da gwamnatinsa.

Gwamnan ya zargi yan adawa kan yade-yaden hotunan da bidiyon dalibai kan yanda suke daukan darasi a jihan don bata wa gwamnatinsa suna.

Badaru ya ga laifin Lamido kan halin da makarantun Jigawa ke ciki
Badaru ya ga laifin Lamido kan halin da makarantun Jigawa ke ciki

Yace gwamnatin tsohon gwamna Lamido ya tsayar da biyan kudade ga hukumar makarantun firamare tun shekara 2013, inda ya kara da cewa al’amarin ya kasance alamun rashin kulawa da gwamnati baya ta nuna.

KU KARANTA KUMA: Yar gaban goshin shugaban kasa Zahra Buhari tayi shar a sabon hoto

Ya kara da cewa duk da kokari da gwamnatinsa keyi don ganin ta magance matsalan, wassu makarantu basu kai ga samun kulawa ba saboda yawan kalu bale da gwamnatin ta sama a kasa.

Da aka tuntube shi, mai Magana da yawun tsohon gwamna Lamido, Malam Kyari Maidamuwa, ya shawarci gwamna Badaru da ya farka daga mafarkinsa.

Maidamuwa yace ya kamata gwamnan ya mayar da hankali kan nuna wa mutanen jihar Jigawa abunda yayi da kudadensu shekaru uku a gwamnatisa maimakon daura wa wani laifi.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng