Gwamnatin tarayya ta fara biyan dubu 5 duk wata ga talakawa a jihar Katsina

Gwamnatin tarayya ta fara biyan dubu 5 duk wata ga talakawa a jihar Katsina

- Gwamnatin tarayya ta ware Naira miliyan 256 domin tallafawa talakawan jihar Katsina

- An fara rabawa talakawan jihar Katsina tallafin Naira dubu 5 duk wata

- Shirin bayar da tallafin na daga cikin alkawuran da jam'iyyar APC ta dauka yayin yakin neman zabe

Gwamnatin tarayya ta saki kudi, Naira miliyan 256, domin rabawa talakawa, Naira dubu biyar, duk wata a jihar Katsina.

Tukur Shehu Ruma, jami'in shirin gwamnatin tarayya na rage radadin talauci ga talakawa a jihar, ya sanar da haka yayin sanya ido a kan yadda rabon kudin ke gudana a karshen satin da ya wuce.

Gwamnatin tarayya ta fara biyan dubu 5 duk wata ga talakawa a jihar Katsina
Buhari da Osinbajo
Asali: UGC

An zabi kananun hukumomi hudu a jihar, daga kowanne yanki, domin fara kaddamar da shirin a jihar. Hakazalika an zabi mazabu uku a kowacce karamar hukuma.

DUBA WANNAN: Sannu a hankali mutuncin Najeriya sai dawowa yake a karkashin mulkin Buhari - Dogara

Jagoran shirin a jihar, Aliyu Isah Girka, ya ce kananun hukumomin da aka zaba sune; Bindawa, Ingawa, Mani, Baure, Musawa, Batagarawa, Rimi, da kaita, a rukunin farko na shirin.

Mutane 21,000 ne ya zuwa yanzu suka karbi nasu kason tallafin, kamar yadda shugaban sashen rabon kudin, Shafi'u Abdullahi Zango, ya tabbatar mana.

Wadanda suka ci moriyar wannan shiri sun nuna farincikin su tare da mika godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, da ya cika wannan alkawari da ya dauka tun lokacin yakin neman zabe.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng