Gurgu ka fi mai ƙafa iya shege: An kama wani gawurtaccen ɗan fashi mai ƙafa ɗaya (Hotuna)
-Yansandan kasar Kwadebuwa sun kama wani rikakken dan fashi da makami
-Dan fashi da aka kama, sunan sa Moussa kuma gurgu ne, mai kada daya
Dubun wani gawurtaccen dan fashi daya dade yana aikata fashi da makami tare da cutar da jama’ar yankin da yake zaune ta cika, inda ya shiga hannun jami’an Yansanda, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Wannan rikakken dan fashi daya shahara na dauke da wani abin mamaki, abin mamakin kuwa shine, dan fashin gurgu ne, wato kafar sa daya, kuma sunan sa Quattara Moussa.
KU KARANTA: Za’a sake ɗiban wasu sabbin hafsoshin rundunar Yansanda – Gwamnatin tarayya
Asirin wannan gurgu ya tonu ne a garin Port-Bouet Jean Foot na kasar Kwadebuwa, a lokacin da wata mata daya taba yi ma sata ta gane shi yayin dayake yawo da tsakar rana.
Yansanda sun kwato makamai da suka hada da bindigu guda 2, dama dai Hausawa sun ce, ai gurgu ya fi mai kafa iya shege. Allah ya shiga tsakanin Nagari da mugu.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng