Illar auren dole: Amarya ta kai ma Angonta mummunan hari sati 3 da yin aure
Wata Amarya da aka yi ma auren dole, Shafa Muhammad mai shekaru 28 ta kai ma mijinta Umar Sheu mummunan hari da reza sati uku kacal da yin aurensu, inji rahoton Daily Trust.
Wannan lamari ya auku ne a daren juma’a 15 ga watan Disamba, a gidan ma’auratan dake Arkilla Liman, cikin karamar hukumar Wammako, a lokacin da mijin yaso yayi mu’amalar aure da Shafa.
KU KARANTA: An yi kare jini, biri jini tsakanin Yansandan Najeriya da masu haƙar ma’adanan ƙasa
Wani shaidan gani da ido ya shaida ma majiyar Legit.ng cewa “Mijin na ta yayi kokarin saduwa da ita ne a lokacin da kai masa hari da reza dake ajiye a gefenta, nan take ta tatstsaga masa kai.”
Kaakakin rundunar Yansandan jihar Sakkawato, Ibrahim Abarass yace tuni aka garzaya da mijin zuwa Asibiti, inda ya samu kyakkyawan kulawa, kuma har an sallame shi.
Kaakakin yace sun kama uwargida Shafa, kuma zasu gurfanar da ita gaban kotu da zarar sun kammala gudanar da bincike akan lamarin. daga karshe ya shawarci iyaye da su guji yi ma yayansu auren dole.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng