Nigerian news All categories All tags
Nollywood: Za a karrama shararren ‘Dan wasa Ali Nuhu

Nollywood: Za a karrama shararren ‘Dan wasa Ali Nuhu

- Za a karrama manyan ‘Yan wasan kwaikwayon Najeriya

- Ali Nuhu yana cikin wadanda su kayi zarra a bana 2017

- Omotola Jalade-Ekehinde tana cikin masu karbar kyauta

Labari ya kai gare mu a karkashin wannan makon cewa ‘Dan wasan Hausa Ali Nuhu yana cikin wadanda ke shirin lashe kyautar ‘Yan wasan kwaiwayo na shekarar nan ta 2017 kwanan nan.

Nollywood: Za a karrama shararren ‘Dan wasa Ali Nuhu

Shararren ‘Dan wasan kwaikwayo Ali Nuhu

Babban ‘Dan wasan kwaikwayon Najeriya Ali Nuhu da kuma Omotola Jalade-Ekehinde da, Lancelot Oduwa Imasuen na cikin wadanda za su lashe kyautar musamman na Nollywood na bana da za ayi a Garin Abeokuta na Jihar Ogun.

KU KARANTA: Mbaka ya marawa Atiku baya wajen takarar Shugaban Kasa

Kowace shekara dai ana kawo ‘Yan wasan fim din da su kayi zarra a fagen wasan kwaikwayo a kasar. Seun Oloketuyi wanda yana cikin wadanda su ka gudanar da wannan kyauta yace ‘Yan wasan sun cancanci a jinjina masu a Kasar.

Mun kuma samu labari cewa tsohuwar ‘Yar wasan Kannywood da aka kora watau Rahama Sadau da kuma Gbenro Ajibade su na cikin wadanda za su karbi lambar yabo a wajen wannan kyauta.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Subscribe to watch new videos

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel