Za'a haramta shan Shisha a Rwanda, shin ko kunsan illar shan shisha kuwa?
Sabon salon samari da 'yan mata, musamman a arewacin Najeriya, shine na shan tabar shisha, a wani tulu mai ruwa, wadda masana suka ce shan ta yafi shan sigari 100 a zama daya. Ita dai tabar shisha anyi ta ne daga siga, wato molasses.
Kasar Rwanda ta tsakiyar Afirka ta haramtawa samari da 'yan mata shan shisha, ta kuma hana shigo da ita daga kasashen waje, saboda illolinta, da ma kuma raguwar kasuwar taba sigari wadda suke da ita a kasar.
Sabon salon samari da 'yan mata, musamman a arewacin Najeriya, shine na shan tabar shisha, a wani tulu mai ruwa, wadda masana suka ce shan ta yafi shan sigari 100 a zama daya. Ita dai tabar shisha anyi ta ne daga shauran siga, ko mazarkwaila, wato molasses a turance.
DUBA WANNAN: Amurka na son kaiwa Iran harin ba-zata
Hukumar lafiya ta duniya ta saki sakamakon bincikenta na cewa tabar shisha din tana da illar shan karan sigari 100 a zama daya, wanda ya sanya gwamnatoci ke ta daukar matakai kan tabar, amma dai a Najeriya babu wanda ya damu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng