Dalibin Makaranta ya kashe abokin karatun sa a cikin daki

Dalibin Makaranta ya kashe abokin karatun sa a cikin daki

- Wani Dalibi ya kashe babban abokin sa a cikin dare

- Ana zargi wani abu ne ya hau kan wannan saurayi

- Yanzu haka an maka Agba a hannun Jami’an tsaro

Mun samu labari mai ban takaici na wani Dalibin Makaranta da ya kashe babban abokin karatun sa a Makarantar gaba da Sakandare ta Polythechnic da ke Jihar Kogi kwanan nan. Dalibin ya cika ne a asibiti bayan an kai shi wajen Likitoci.

Wannan dalibi mai suna Akoh Samuel Abuh ya bakunci lahira ne bayan da babban abokin sa a Makarantar ya daba masa adda. Wadannan samari dai su na karatun babbar difloma ne na HND a Makarantar koyon aikin da ke Garin Kogi.

KU KARANTA: Gwamnan Jihar Bauchi ya yabawa aiki Mai dakin Shugaban Kasa

Har yanzu dai an rasa gane asalin abin da ya faru da wannan dalibi mai suna Agba da ya kashe abokin kwanan nan sa. Amma dai mun ji cewa yanzu haka an maka shi ofishin binciken masu manyan laifuka na ‘Yan Sanda watau CID na Garin Kogi.

Hukumar Makarantar ta bayyana mana cewa tun kafin abin ya faru aka fahimci cewa wannan ‘Dalibi ya fara samun matsala a kan sa don haka ne ma aka kai shi coci domin addu’a. A Ranar Talata da dare ne dai ya gwabje Samuel da makami.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng