Wani asararre ya sassara matarsa da adda kan ta hana shi a kan lokaci
Wani Maigida mai shekaru 50 ya fada komar Yansanda a jihar Neja, Tanko Bamaiyi bayan ya jirge matarsa, Auta da adda, har ta mutu, wai don saboda bata kammala girki ba, don haka bata ba shi abinci a kan lokaci ba.
Rariya ta ruwaito wannan lamari ya auku ne a lokacin da cacar baki ta kaure tsakaninsu, inda Mijin ke ma matar tasa fada cewa kwanaki biyar kenan bata ba shi abinci ba, daga nan ya dauko adda ya sassara mata, nan take ta fadi matacciya.
KU KARANTA: Illar cin hanci: Sojan Najeriya ya bindige wani Mahauci a kan ya hana shi N500 na goro
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Mijin ya tabbatar da kisan matar tasa, amma yayi nadamar abin ya aikata. “Kulluma bata bani abinci akan lokaci, kuma idan na yi mata magana, sai ta zazzage ni, har ma ta kai ga idan na tambayi abinci, har yar mu mai shekaru 10 sai ta zage ni. Amma na yi nadamar abin da na yi, kuma ina neman afuwa daga wajen surukai na.”
A nasa jawabin, Kaakakin rundunar Yansandan jihar Neja, Peter Sunday ya bayyana cewa zasu gurfanar da mutumin gaba Kotu bayan sun kammala bincike.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng