Akwai kishin-kishin din Neymar zai koma Real Madrid
- Real Madrid na iya sayen Neymar daga Kungiyar PSG
- Kwanan nan Kungiyar Barcelona ta rabu da ‘Dan wasan
- Idan ta tabbata cinikin zai girgiza Duniyar kwallon kafa
Za ku ji cewa yanzu tsohon Dan wasan Barcelona watau Neymar Jr. na iya komawa Real Madrid daga Kungiyar PSG ta Faransa kwanan nan. Shekarun baya Madrid sun taba dauke babban Dan wasan Barcelona Luis Figo.
Kungiyar Real Madrid na iya sayen babban Dan wasan Duniya Neymar daga PSG kan wasu makudan kudi da ya haura yadda PSG ta saye shi nan gaba kamar yadda rahotanni daga Kasar Sifen ke yawo tun kwanakin baya.
KU KARANTA: Kungiyar Real Madrid na shirin kara cin wani muhimmin kofi a 2017
Neymar ne ‘Dan wasan da ya fi kowa tsada a Duniya bayan da ya bar Barcelona zuwa PSG a bana. Barcelona ta saida ‘Dan wasan da ta fi ji da shi bayan Lionel Messi watau Neymar ne a kan kudi sama da $200 ba don ta na so ba.
Sai dai watakila Real Madrid ta zagaya ta baya ta nemi ta saye ‘dan wasan da ta dade tana sha’awa. Har ta kai ‘Yan wasan Barcelona sun fara gudun yiwuwar wannan ciniki. An dai taba yin haka da Dan wasan Barcelona Luis Figo a baya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng