Da yawa cikin 'yan Najeriya da suka dawo daga Libya na fama da tabin hankali - IOM

Da yawa cikin 'yan Najeriya da suka dawo daga Libya na fama da tabin hankali - IOM

- Shugaban ofishin jakadancin Najeriya na kungiyar IOM tace wasu daga cikin yan Najeriya da suka dawo daga Libya na fama da tabin hankali

- Shugaban tace bayan an basu kulawa na musamman da shawarwari, kungiyar zata taimaka masu domin su samu abin yi

- Shugaban kuma tayi kira ga gwamnatin Najeriya ta taimaka musu da tallafi domin abin da suke samu daga kasashen ketare baya isa

A jawabin bude taro da tayi a garin Akwanga da ke Jihar Nasarawa, shugaban kungiyar kasa da kasa na 'yan hijira IOM, Enira Krdzalic tace kungiyar nasu tayi nasarar bada kulawa na shawarwari ga 'yan najeriya da suka dawo daga Libya musamman wanda suke fama da tabin hankali.

Da yawa cikin 'yan Najeriya da suka dawo daga Libya na fama da tabin hankali - IOM
Da yawa cikin 'yan Najeriya da suka dawo daga Libya na fama da tabin hankali - IOM

Krdzalic wanda ta samu wakilcin shugaban hukumar tsare-tsare na kasa, Mista Sunday Omoyeni tace cikin sama da mutane 5000 da suka dawo daga Libya, kungiyar har yanzu bata kammala mayar da su cikin al'umma ba domin suna bukatan kulawa wanda matakin farko shine basu shawarwari.

KU KARANTA: Za'a a ga ba daidai ba idan wani abu ya faru da Magu - Kungiyar MURIC

Tace mafi yawancin su basu da lafiya, wasu ma suna fama da tabin hankali hakan yasa a ka tura su asibitin masu fama da tabin hankali. Daga baya kungiyar zata basu horo domin su samu sana'ar yi.

Ta kara cewa suna bukatan taimako daga gwamnatin Najeriya domin tallafin da kasashen ketare ke bayar wa baya isa kuma idan a ka bar su ba tare da sana'a ba zasu zama fitina ga kasa baki daya.

A cewar Krdzalic, tsakanin Janairu da Nuwamba na 2017, kungiyar IOM ta taimaka wajen kula da 'yan Nijeriya 4,489 wanda suka dawo daga kasar Libya kuma a hain yanzu wasu suna kan hanyar dawowa.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164