An kama barayin Motoci da kuma yan fashi da makami a jihar Kebbi
- Jami'ain yansada sun kama barayin motoci a jihar Kebbi
Kwamishinan yansadar jihar Kebbi ya ce sun kama yan fashi 41 da kwato makamai 12 daga hannun su
- Kabiru Ibrahim yayi kira da mutanen jihar Kebbi da su rika ba jami’an tsaro hadin kai dan kawar da bata gari
Kwamishinan yansadar jihar Kebbi Kabiru Ibrahim yace rundunar su ta kama yan fashi 41 da kwato makamai 12 daga hannun su a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba a Kebbi.
Kabiru Ibrahim yace yanzu haka yan fashi suna tsare a kurkuku, kuma za su cigaba da zama a kurkuku har sai kotu ta gama sauraron karar su.
Ibrahim ya kara da cewa, rundunar su ta kama barayin motoci da kwato motoci shida 6, da babura guda goma sha bakawai 17 sannan sun shigar da su kara kotu.
KU KARANTA : Farashin dala ya dawo N314.50 akan naira, tsakanin bankuna
“Kuma sun mayar da garken shanu guda 131 da suka kwato daga hanun barayin shanu zuwa ga hannun masu shi”.
Kwamishinan yayi kira da mutanen jihar da su rika ba jami’an tsaro hadin kai dan kawar da bata gari a jihar su.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng