Alheri gadon barci: Halayyar kirki da wani mutumi ya nuna ma wata Zakanya ya sa sun shaƙu da juna
Wani abun ban mamaki ya faru a birnin Mexico, inda wani abun da ba’a saba gani ba ya faru a tsakanin wani mutumi mai suna Adolfo da kuma wata gagarumar Zakanya.
Zakanyar da aka yi ma suna da ‘Kiara’ ta dira kan Adolfo daga ganinsa cikin yanayi irin na rungumar Soyayya, sakamakon halin kirki da tausayi da ya nuna mata a lokacin da take cikin mawuyacin hali a baya.
KU KARANTA: Girma ya faɗi, wani Sanata daga majalisar dattawa ya koma harkar waƙoƙin zamani
Daily Mail ta ruwaito Adolfo ne mutumin daya fara kiwon Kiara, daga bisani kuma bayan ta fara girma aka kai ta gidan ajiyan namun daji mai suna ‘Black jaguar White Tiger Foundation’ don samun ingantaccen kulawa.
Wannan ne dalilin da yasa Kiara ba zata ta manta da Adolfo ba, yasa a kullum ta ke shaukin ganin tsohon Maigidan na ta, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.
Da wannan ake jan hankalin mutane da su dinga tuna alheri, tun idan har a ce dabba ba ta manta alheri, tabbas mutum ne ya fi dacewa kada ya manta alheri.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng