Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano

Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano

- Adam Zango yayi bukin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwasko a Kano

- Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi da Fati SU, sun halarci bukin

- Zango ya karrama masoyansa da suka halarci bukin da kyaututtuka

Shaharrren dan wasan kwaikwayon Kannywood Adam A Zango, ya karrama masoyan sa dake garin Kano a lokacin bukin shirrin kaddamar da sabuwar fim din sa mai suna gwaska Return da zai fito a ranar 1 ga watan Janairu na shekara 2018.

Adam A zango yayiwa masoyansa da suka halarci bukin kyaututuka da ya kunshi riguna, huluna da sauran su.

Jarumai kamar Ali Nuhu, Nafisa Abdullhi Fatu SU, sun halarci bukin a birnin Kano.

Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano
Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano

Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano
Adam Zango ya karrama masoyan sa a Kano

Daya daga cikin hadiman Zango, mai suna Mansur Make-Up, ya bayyana wa yan jarida cewa Adam Zango ya shirya bukin ne domin nuna ma masoyar sa irin kaunar da yake musu.

KU KARANTA: An shiga rudani a jihar Ondo yayin da rikici ya barke tsakanin yansanda da sojoji

Jaruma FatI Su ta shaidawa yan jarida cewa Adam Zango mutum ne mai matukar kaunar jama’a, kowa nasa ne, kuma abun da yayi wa masoyan sa abun ne da ya cancanci yabo ne.

Mutum ne dake da matukar kyauta da taimako. Har mu ma jaruman fim bai bar mu wajen ganin cewa mun samu daukaka a masana’artar fim.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng