Jirgin mata zalla na farko zai sauka Najeriya daga kasar Habasha
Ana sa ran saukar jirgi mai dauke da mata zalla a Najeriya a ranar Asabar. Jirgin ya kasance na kasar Habasha wato Ethiopian Airlines.
A cewar kungiyar kamfanin jirgin sama, mata zasu cike dukka nmatakai a jirgin; abinda ya kama daga matuka da ma’aikatan cikin jirgin, har da masu aikin kula da gangarar jirgin da masu balaguro a kasar.
Wannan zai kasance karo na farko da ET zata gudanar da aikin jirgi na mata zalla a Afirka.
A wani jawabi da aka kaddamar a Legas, kamfanin jirgin saman tace jirgin zai tashi daga Addis Ababa, babbar cibiyar ayyukan jirage, a ranar 16 zuwa tashar jirgin Murtala Muhammed International Airport (MMIA), dake jihar Legas.
Matukiyar jirgin, Captain Amsale Gualu, ta yi tukin jirgi zuwa sauran yankuna a baya.
KU KARANTA KUMA: Mataimakin shugaban kasa ya jagoranci zaman majalisa (hotuna)
Jirgin mata zallan na da Tigist Kibret a matsayin matukiyar ta na farko, wacce zata tuka jirgin mai suna Boeing 777.
A kasar inda mata kalilan suka shiga sana’an tukin jirgin sama wacce mafi yawanci maza ne, Captain Gualu, a 2010 ta kasance mace ta farko a kasar Habasha da tayi tuki daga Addis Ababa zuwa Gondar.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng