Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ya sha da kyar a hannun a Jama’a

Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ya sha da kyar a hannun a Jama’a

- Tsohon Gwamnan Borno ya sha da kyar a hannun a Jama’a

- Mutanen Gari sun nemi su yi Ali Sheriff mugun duka a gida

- Sai da ‘Yan Sanda su ka sa hannu aka ceci tsohon Gwamnan

Dazu mu ka ji cewa tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Ali Modu Sheriff ya sha da kyar a hannun Jama’an gari bayan da ya kai ziyara a Jihar Borno inda aka yi wani taro ana addu’o’i.

Tsohon Gwamnan Borno Ali Modu Sheriff ya sha da kyar a hannun a Jama’a
Sanata Ali Modu Sheriff ya gamu da fushin matasa
Asali: Facebook

Tsohon Gwamnan na Jihar Borno Ali Sheriff ya sha da kyar ne a hannun fusatattun Matasan Garin yayin da su kayi kokarin yi masa dan-karen duka kamar yadda wani bidiyo da gidan yada labaran nan na Sahara Reporters ta saki ya nuna.

KU KARANTA: Yadda na zama Gwamna ban da ko sisi a 2007 - Amaechi

Mutanen Borno na zargin tsohon Gwamnan na su Sanata Ali Modu Sheriff da hannu dumu-dumu a cikin rikicin Boko Haram wanda yayi sanadiyar mutuwar dinbin Jama’a. Ba mamaki hakan ya sa wasu ke jin haushin tsohon Gwamnan.

Abin dai ta kai da sai da Jami’an tsaro na ‘Yan Sanda su ka lalubo bindiga don kuwa wasu sun yi niyyar jibgar mai girma tsohon Gwamnan. Har yanzu dai Ali Sheriff bai ce komai ba bayan wannan takaddama da ta faru kwananan nan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng