Kudin haram baya albarka: Tsohon kwamishinan Yansanda ya ja kunnen jami’an Yansanda
Wani tsohon kwamishinan Yansandan jihar Anambra, Nwachukwu Egbochuku ya danganta tsananin talauci da ke damun Yansandan Najeriya da irin silar dukiyar da suke Tarawa.
Daily Trust ta ruwaito tsohon kwamishinan yana fadin da dama daga cikin Yansanda na tara arzikinsu ne ta hanyar haram, wanda hakan ke sa dukiyarsu bata albarka, sai su yi ta rayuwa a tsiyace.
KU KARANTA: Yaki da rashawa: Tsohon gwamnan jihar Kebbi zai bayyana a gaban Kotu
Egbochuku ya bayyana haka ne a garin Awka na jihar Anambra a ranar Talata 12 ga watan Disamba, inda yace wannan ne dalilin da yasa zaka ga da zarar Dansanda yayi murabus, sai kaga duniya ta yi masa daurin demon minti, saboda irin ta’asar daya tafka yayi dayake aiki.
“ Na san wani DPO dake aika Yansanda da motar Bas, inda suke cika ta da mutane kamar wata motar haya, sai su wuce da su caji ofis, inda sai kowa yayi belin kan sa kafin ya tafi. Haka zalika akwai wani babban jami’in Dansanda da na sani, wanda yake aika kananan Yansanda suna kashe duk wanda ya so, amma fa a wulakance ya kare rayuwarsa.” Inji Egbochuku.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito tsohon jami’i yana shawartar gwamnati da ta kara yawan kudaden da ake ware ma rundunar Yansanda a kasafin kudin shekara shekara, ko hakan zai rage yiwuwar Yansanda su cigaba da tafka ta’asa iri iri da nufin samun kudi.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng