Makarantar Sheikh dahiru Bauci ta yaye mahaddatan Al'kur'ani 898
Kimanin dalibai 898 ne a halin yanzu suka kammala haddar Al-Kur’ani mai girma a makarantun babban shehin malamin addinin Islamar nan kuma jagoran marhabar Darikar Tijjaniyya, Sheikh Dahiru Usman Buchi sannan kuma wasu 312 sauke ba ta hanyar handaccewa ba a fadin kasar nan.
Darakta Janar din dake kula da harkokin ilimi a wata Gidauniyar ta Shehin malamin dake kuma zaman da ga Malamin mai suna Sheikh Sidi Aliyu Sise Dahiru Usman Bauchi da kuma Malam Hassan Adam ne suka bayyana hakan a yayin jawaban su daban daban lokacin da ake yaye wasu daliban a jihar Bauchi.
KU KARANTA: Zamu gama da Boko Haram cikin karamin lokaci
Legit.ng dai ta samu cewa Sheikh Sidi Aliyu Sise ya ce wannan adadin na daliban sun fito ne daga wasu makarantun dake a rassa daban-daban a jihohin Kebbi, Bauchi, Kano, Kwara, Kaduna , Adamawa, Sokoto, Zamfara,Gombe da kuma jihar Neja.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa a kwanan baya mun ruwaito maku cewa Shehin malamin yana wata rashin lafiya inda kuma aka nemi jama'ar musulmi da su taimaka masa da addu'o'i.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng