Tawagar Shugaban Kasa ta isa Birnin Faris domin halartar babban taro

Tawagar Shugaban Kasa ta isa Birnin Faris domin halartar babban taro

- Shugaban Kasa Buhari ya isa babban Birnin Kasar Faransa

- Gwamnonin Kano da Adamawa da Ondo su na cikin tafiyar

- Najeriya za ta halarci wani muhimmin taro na yini huda gobe

Dazu nan mu ka ji cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya isa babban Birnin Kasar Faransa watau Faris. Tawagar Shugaban Kasa ta isa lafiya inda Najeriya za ta halarci wani babban taro na Kasashen Duniya da za ayi a gobe.

Tawagar Shugaban Kasa ta isa Birnin Faris domin halartar babban taro
Shugaban Kasa Buhari tare da Gwamnan Ondo ana gaisawa

Kamar yadda Fadar Shugaban Kasar ta saki hotuna da bidiyo, an ga Buhari yana saukowa daga jirgin Kasar inda Gwamnoni da sauran wadanda su ke cikin tafiyar su ke yi masa maraba da zuwa. Shugaban Kasar ya tashi ne ta Garin Kano dazu.

KU KARANTA: Osinbajo ya shiga taro da Sarakunan Najeriya a Fadar Villa

Gwamnonin da su ke cikin tafiyar dai su ne Gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje da kuma Gwamnonin Adamawa da na Jihar Ondo Bindow Jibrilla da Rotimi Akeredolu. Saura sun hada da Ministocin muhalli da na harkokin kasar waje.

Dazu kun ji cewa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya sa labule da Sarakunan Arewa yayin da shi kuma Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bar Najeriya ya isa Kasar Faransar a wannan lokaci. Shugaban Kasar dai ya leka Daura kafin ya bar Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng