Ko ka san wacece matar Adams Oshiomole da ake ta magana a gari?
- Mun kawo maku abubuwa 3 game da labarin Uwargidar Adams Oshiomole
- Tsohon Gwamna Adams Oshiomole ya auri Lara ne bayan rasuwar matar sa
- Adams Oshiomole ya girmi Lara ta sa nesa ba kusa ba don kuwa ya sha miya
Kwanakin baya Adams Oshiomole ya auri wata Budurwa da ake ta surutu. Jama’a da dama na ta tambaya game da Mai dakin ta tsohon Gwamna Jihar Edo Oshiomole. Oshiomole ya rasa matar sa da yake ji da ita shekarun baya.
Mun kawo maku tarihin Mai dakin tsohon Gwamnan Jihar Edo da ake ta maganar ta a gari mai suna Lara wanda tsohon Gwamnan ya aura ana daf da rantsar da Muhammadu Buhari Shugaban Kasa a farkon shekarar 2015.
KU KARANTA: Gwamnan Legas yace karfi yayi wa Gwamnatin Tarayya yawa
1. Asali dai Mahaifin wannan Budurwa da tsohon Gwamnan ya aura ‘yar Kasar Cape Verde ce ko da yake Mahaifiyar ta ‘Yar Najeriya ce.
2. Lara Oshiomole tayi aiki a jirgin sama na Emirate Airlines kuma asalin ta dai Lauya ce sannan ta kware a sana’ar kwalliya da gayu.
3. Oshiomole ya girmi sahibar ta sa da ya aura tana danyar budurwa da shekaru kusan 30 da haihuwa. An daura masu aure ne a Ranar 15 ga Watan Mayun 2015.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng