Wani malalacin Maigida ya gamu da fushin Uwargida, ta kwance masa zani cikin kasuwa
Wata Uwargida ta bude ma mijinta aiki a gaban Kotu bayan kwashe shekaru goma suna tare, inda ta bukaci Alkalin Kotun ya raba aurensu, saboda shi mijin nata malalaci ne, baya son zuwa aiki.
Uwargida Awawu ya roki Kotun gargajiya dake Igando, jihar Legas, da tayi ma Allah ta raba aurenta da Ibrahim Oseni, wanda ta ce baya kaunar zuwa aiki, don haka baya ma iyalinsa amfanin komai, inji rahoton kamfanin dillancin labaru, NAN.
KU KARANTA: Tawagar babban hafsan sojan kasa Tukur Buratai ta yada zango a fadar gwamnatin jihar Oyo
“Malalacin baya zuwa aiki, barci yake shara tun daga safe har yamma, sai tsabar minsha kamar rago, tun bayan aurenmu yake min karya, har yanzu mahaifiyata ke biya mana kudin haya, tare da ciyar da mu. Kuma ban taba hana shi abinci ba, saboda daga yaji yunwa sai duka.” Inji Awawu
Awawu ta cigaba da shaida ma kotu yadda mijinta ke ci mata mutunci cikin mutane, yana kiranta da sunan karuwa ko karya, don haka ta ke yi ma kotu ma magiyar a raba ta da shi, idan ba haka ba, zai kashe ta wata ran.
Sai dai Ibrahim ya musanta zarge zargen matar, inda yace tana bin maza ne, wannan shine matsalar ta da shi, “Ina zargin mata ta tana bin maza ne, don haka idan ta dawo, na tambayeta wajen wa ta je, sai ta ki, ni kuma sai na jibge ta son rai na.”
Haka zalika ya musanta wai shi Malalaci ne, inda yace “Duk da cewa ina zama a gida tun safe, amma yamma na yi zan fita da babur don yin aikin acaba”, don haka shi kuma ya roki kotun da kada ta raba aurensa da matarsa, don har yanzu yana son abin sa.
Bayan sauraro dukkan bangarorin biyu, sai alkali Moses Akinniyi ya dage sauraron karar zuwa 18 ga watan Disamba don cigaba da sauraro.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng