Nasir El-Rufai da matarsa sunyi shar a sabbin hotuna
- An gano gwamnan jihar Kaduna da amaryarsa cikin raha a wani taro
- An gano Gwamna El-Rufai da amaryarsa Asia, suna dariya da farin ciki a wasu hotuna
An gano Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai na jihar Kaduna tare da kyakkyawar matarsa, Asia El-Rufai a wajen wani taro.
Ma’auratan biyu sun kasance cikin nuna wa junan su tarin soyayya a wajen taron. An gano su suna dariya a tare a wajen taron.
An gano El-Rufai sanye cikin shadda dinkin babban riga kalar toka daga sama har kasa yayinda matar tasa ke sanye da atampa kore da launin ruwan kasa.
Gwamna El-Rufai ya zamo gwamnan jihar Kaduna a shekarar 2015 sannan kuma yana da kyawawan matan aure guda uku, Ummi, Hadiza da kuma Asia.
KU KARANTA KUMA: 2019: Babu wani dan arewa a doron kasa da zai iya kayar da Buhari – Lauretta Onochie
Haka zalika Allah ya albarkaci gwamnan da kyawawan yara guda biyar.
El-Rufai ya rike mukamai da dama a kasar kafin ya zamo gwamna.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng