Yara dubu 170 ke hawa yanar gizo a kullum - UNICEF ta yi gargadi
- UNICEF ta yi kira da kwararru a fannin Intanet da su samar da sabin hanyoyin da zai kare kananan yara da ke amfani da yanan gizo saboda kada tarbiyan su ya gurbata
- Hukumar UNICEF ta yi kira dai iyaye su rika sa ido akan yadda yayan su ke amfani da yanar gizo
Hukumar kula da kananan yara karkashin majalisar Dinkin Duniya UNICEF, ta yi kira da kwararru a fannin sada zumunta na zamani da su dauki matakan da za kare kananan yara da ke amfani da yanan gizo.
Hukumar UNICEF ta ce ana samun yara sama da dubu dair da saba’in da suke amfani da yana gizo a kowace rana a duniya.
UNICEF ta ce akwai bukatar fitowa da sabbin hanyoyin kare kananan yaran dake amfani da yanan gizo dan hana su shiga shafikan da zai gurbata tarbiyan su.
KU KARANTA : Kaso 89 na yan Najeriya na cikin bakin ciki - Okorocha
Kuma hukumar UNICEF ta yi kira dai iyaye su rika sa ido akan yadda yayan su ke amfani da yanar gizo.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng