Kannywood sun yi fim din Maryam Sanda da Bilyaminu marigayi
Fostar fim din, ta nuna wata mata da jajayen kaya ta caka wa wani saurayi wuka lokacin yayi sujjada a sallah. Wasu na ganin yin fim din bai dace ba musamman ganin yadda batun ke gaban kotu. Wasu kuma na ganin ma tunda wani ya rasu, bai kamata wasu su ci kudi da hakan ta hanyar fim ba.
Fim din ta kashe shi, fim ne da Jamilu Ahmad Yakasai ya shirya, kuma har sun fara sayar dashi a kasuwa.
A labarin dai, kamar yadda aka ji a gaske, wata mata ce tsananin kishi ya sanya ta kashe mijinta yana cikin sallah, saboda zai karo mata kishiya.
Masu hada fim din na fata ne su fadakar da jama'a kan mugun kishi da abin da zai tarwatsa ma mutum rayuwa.
DUBA WANNAN: Abubuwa da suka faru a 2017
A waje daya kuma, wasu na gani tunda batun yana kotu, bai kamata ayi fim din ba, ko ma kuma cewa wani ya rasa ransa a gaske, bai kamata ayi ffim a ci riba dashi ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng