An bayyana yariman Saudiyya a matsayin wanda ya sayi hoton Yesu a kan dala miliyan 450

An bayyana yariman Saudiyya a matsayin wanda ya sayi hoton Yesu a kan dala miliyan 450

- Dan sarkin Saudiyya ya sayi hoton Yesu a kan farashi mai tsada

- Yariman na Saudiyya na kokarin kawo canji a tsarin mulkin kasar

- Kasar Amurka na bibiyar al'amuran Yariman

Yariman kasar Saudiyya, Mohammed bin Salman, ya sayi wani zanen hoton Yesu Almasihu da shahararren mai zane dan kasar Italiya, Leonardo da Vinci, ya zana a kan farashin Dala miliyan 450, kamar yadda jaridar The Wall Street Journal ta rawaito.

Yariman da aka fi sani da takaitaccen sunan sa MBS ya yi amfani da wani a tsakiya wajen sayen zanen ganin cewar kasar Amurka ta sanya idanu a kan al'amuran Yariman.

An bayyana yariman Saudiyya a matsayin wanda ya sayi hoton Yesu a kan dala miliyan 450
An bayyana yariman Saudiyya a matsayin wanda ya sayi hoton Yesu a kan dala miliyan 450

Ana ganin Yariman na Saudiyya a matsayin mai sassaucin akidar Islama tare da yunkurin kawo canji a tsarin mulkin Saudiyya na tsatstsauran ra'ayin addinin Islama.

DUBA WANNAN: Shinkafar kasan waje da ke Najeriya sumogul dinsu akayi, galibinsu gurbatatu ne - Gwamnatin Tarayya

Wata majiya ta bayyana cewar kasar Amurka na bibiyar al'amuran Yarima Mohammed bin Salman, kamar yadda rahotanni suka wallafa.

A ranar Laraba birnin Abu Dhabi na kasar Dubai ta bayyana cewar za a ajiye shi a wani wurin yawon masu bude ido.

Zanen hoton na Yesu da Leonardo da Vinci ya yi nada shekaru kimanin 1500 duk da wasu sun ce ba asalin zanen Yesu da Leonardo da Vinci ya yi ba ne.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164