‘Yan Boko Haram sun kashe wani gwarzon Soja a Maiduguri
- ‘Yan Boko Haram sun yi wa Rundunar Sojin Najeriya barna
- An kashe wani barden Soja yana shirin zama Ango kwanan nan
- Kamal ya dade a Garin Maiduguri yana fama da ‘Yan ta’adda
Dazu mu ka ji labari daga shafin Support Nigerian Military cewa wani Sojan Kasar nan da ke shirin aure ya rasa ran sa wajen yaki da ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garin Maiduguri kwanan nan.
An yi rashin wani namijin Sojan ne mai suna Kamal yayin da yake gwabzawa da ‘Yan ta’addan Boko Haram a Garin Maiduguri da ke Jihar Maiduguri inda har yanza ake fama da ragowar ‘Yan ta’addan na Boko Haram.
KU KARANTA: Yaron da Boko Haram su kayi wa rauni tashi da kafafun sa
Kamar yadda labarin ya zo mana wannan Bawan Allah ya cika ne yayin da yake daf da shirin zama Ango. ‘Yan uwan sa dai sun koka da rashin wannan gwarzo da Allah bai yi zai samu yin aure kafin ya bar Duniya ba.
Har yanzu dai ana cigaba da rasa tsirarrun Sojojin Najeriya a hannun ‘Yan Boko Haram a kasar. Kwanan nan ne Sojoji su ka damke wani yana shirin dasa bam a Garin Maiduguri wanda tuni aka yi ram da shi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng