An sake dawo da 'yan Najeriya 257 daga kasar Libya
- Wasu mutane da adadin su yakai 257 sun sake dawowa Najeriya daga kasar Libya
- Yawanci mutanen sunce sun tsinci kansu ne a kasa Libyan a hanyar su na ketare iyaka domin shiga nahiyar turai
- Ma'aikatan harkokin kasashen waje na Najeriya tace zata cigaba da jigilan yan Najeriyan da ke tsare a kasar ta Libya domin dawo dasu gida
Jim kadan bayan 'yan Najeriya 144 sun dawo daga kasar Libya, wani jirgin ya sake sauka a filin tashin jirgi na Murtala Mohammed da ke Legas dauke da mutane 257 a ranar Laraba.
Mai magana da yawun shugaban yan sanda masu kula da filin tashin jirgin, Joseph Alabi ya tabbatar da wannan labarin a hirar da yayi da kamfanin dilancin labarai NAN.
Mr Alabi yace mutanen sun iso Legas ne a cikin jirgin kasar Libya misalin karfe 1.30 na safiyar yau da taimakon kungiyar IOM da kuma kungiyar hadin kan kasashen turai, EU bayan sun tsinci kansu a kasar ta Libya a hanyar su na zuwa kasashen turai.
Yace cikin mutanen da suka dawo, 65 mata ne, 179 manya maza, sannan akwai kananan yara 7 da kuma jarirai 6. Ya kuma ce akwai mutane 4 da ke fama da rashin lafiya wanda tuni an garzaya dasu asibiti domin yi musu magani.
KU KARANTA: Trump ya bayyana niyyar sa na mayar da ofishin jakadancin Amurka zuwa Jerusalem
Kamar yadda ya bayyana, Jam'an hukumar bada agajin gagawa ta NEMA, FAAN, da hukumar yaki da safaran mutane na kasa ne suka karbe su.
Sauran mutanen da ke cikin tawagar tarban nasu harda Uwargidan Shugaba Buhari, Aisha Buhari wadda ta samu wakilcin Uwargidan gwamnan Jihar legas, Bolanle Ambode, da kuma mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin kasashen waje, Abike Dabiri Erewa da kuma wasu manyan jami'an gwamnati.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun Ma'aikatar harkokin kasashen waje, Tiwatope Elias-Fatile tace Najeriya tana cigaba da ziyarar wuraren da aka tsare 'yan Najeriya a kasar Libyan domin yi musu rajista sannan a dawo dasu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng