Na kirkiro ma'aikatar walwala da farinciki ne domin magance kunci da bakin ciki - Okorocha

Na kirkiro ma'aikatar walwala da farinciki ne domin magance kunci da bakin ciki - Okorocha

- Jihar Imo ta kirkiri ma'aikatar walwala da farinciki

- Gwamna Rochas ya nada wata 'yar uwar sa a matsayin kwamishiniyar ma'aikatar

- Ya ce kirkirar ma'aikatar zai rage rayuwa cikin kunci da bakin ciki

Gwamnan Jihar Imo, Rochas Okorocha, ya bayyana cewar ya kirkiri ma'aikatar walwala da farincikin al'umma ne bayan nazarin mutanen jihar sa.

Rochas ya bayyana hakan ne a wata takarda da sakataren sa na yada labarai, Mista Sam Onwuemeodo, ya raba ga manema labarai a jihar.

Na kirkiro ma'aikatar walwala da farinciki ne domin magance kunci da bakin ciki - Okorocha
Rochas Okorocha

"Kasancewa cikin farinciki abu ne mai muhimmanci ga rayuwa. Ko jama'a na zaben shugannin da suke ganin zasu saka su farin ciki ne. Babu aiki mafi muhimmanci a rayuwa irin ka sanya mutum farin ciki". A jawabin gwamnan.

DUBA WANNAN: Sun bindige shi har lahira ranar da yake binne Mahaifiyar sa

Jawabin ya ci gaba da cewa "Abin takaici ne cewar bamu bawa bangaren walwala da farinciki muhimanci ba a gwamnatance. Kokarin gwamnati, a baya, na saka jama'a farin ciki ya gaza. Mutane da yawa a Najeriya basa iya cimma burin su saboda kunci da bakin ciki da ya addabi rayuwar su".

Hakazalika gwamna Rochas ya ce ko a jami'a, dalibin da ya karanta abinda ke saka masa farin ciki ya fi kwazo, tare da bayyana cewar ya kirkiri ma'aikatar ta walwala da farincikin al'umma domin inganta rayuwar mutanen jihar Imo.

A jiya ne dai gwamna Rochas ya yi sabbin nade-naden kwamishinoni tare da nada wata 'yar uwar sa a matsayin kwamishina a ma'aikatar walwala da farincikin al'umma.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng