Ziyarar Buhari jihar Kano za ta yi tasiri matuƙa – Inji Sanata Barau Jibrin
Sanata Barau Jibrin ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai samu tagomashin cimma wasu muhimman abubuwa guda hudu ta hanyar ziyarar da zai kai jihar Kano.
Ana sa ran shugaba Buhari zai kaddamar da mayna ayyuka, tare da sanya tubalin ginin wasu ayyukan na daban, a yayin ziyarar da zai kai jihar Kano, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
KU KARANTA: Hotuna wasu jarirai 2 da aka jefar, ɗaya cikin kwali, ɗaya cikin baƙar Leda a Kebbi
Daily Trust ta ruwaito Sanata Barau yana fadin cewa ziyarar zata baiwa shugaba Buhari daman nuna godiyarsa ga jama’an jihar Kano, sakamakon miliyoyin kuri’un da suka tula masa a zaben 2015.
Abu na biyu a cewar Sanatan shine, ziyarar zata bashi daman jin matsalolin al’umman jihar Kano, tare da sauraron shawarwari daga bakunansu, musamman tun da dai zai gana da masu ruwa da tsaki na jihar.
Sanatan ya cigaba da fadin amfanin ziyarar shugaba Buhari jihar Kano, inda ya kara da cewa ziyarar zata baiwa shugaban kasa daman bayyana ma al’ummar Kano ire iren abubuwan da ya aikata musu.
Abu na karshe kuma shine, ziyarar zata kara dankon zumunci dake tsakanin shugaba Buhari da Kanawa, wanda yace, tsohon danganta ne ke tsakanin su, “Baya da Daura, babu inda ake kaunar Buhari kamar Kano.” Inji Barau.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng