Siyasa kasuwanci ne ga yawancin yan siyasan Najeriya - Wabba
- Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya (NLC), Kwamrad Ayuba Wabba ya bayyana cewa siyasar Najeriya yafi kama da kasuwanci
- Kwamrad Wabba yayi kira ga a kara wayar wada yan siyasa kai
- Ya yi tsokacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wata kungiyar jama’a mai suna Say No Campaign Nigeria
Shugaban kungiyar kwadago na Najeriya (NLC), Kwamrad Ayuba Wabba ya bayyana cewa siyasar Najeriya yafi kama da kasuwanci.
Kwamrad Wabba yi tsokacin ne a lokacin da ya karbi bakuncin tawagar wata kungiyar jama’a mai suna Say No Campaign Nigeria a ofishin sa dake babban birnin tarayya Abuja, a ranar Talata, 5 ga watan Disamba.
Shugaban kungiyar kwadagon ya bayyana cewa babban matsalar Najeriya shine shugabanci, inda ya kara da cewa akwai bukatar a sauya tsarin siyasar kasar.
KU KARANTA KUMA: Gwamna Ganduje ya kwana aiki domin tarbar Shugaba Buhari
Ya yaba ma tawagar kungiyar ta Say No Campaign bisa jajircewarsu a shekaru da suka gabata, inda ya kara da cea kungiyar kwadago na mutuntasu sosai.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng