Maikanti Baru ya rugo ya dawo Najeriya domin dakile matsalar wuyan man fetur

Maikanti Baru ya rugo ya dawo Najeriya domin dakile matsalar wuyan man fetur

- Maikanti Baru ya gaggauta ya dawo Najeriya domin dakatar da matsalar karancin man fetur

- Ya hakura da karbar kyautar da za bashi a kasar Ingila

- An fara layuka a gidajen man fetur dake fadin Najeriya

A kokarin sa na ganin cewar karamar matsala bata zama babba ba, babban darektan kamfanin man fetur na kasa, Maikanti Baru, ya rugo daga kasar Ingila ya dawo Najeriya domin dakile matsalar wuyan man fetur da ta fara kunno kai karshen satin da ya wuce.

Dakta Baru ya yi wata tafiya ne ya zuwa kasar Ingila domin karbar kyautar da jaridar Forbes ta kasar ta bayyana za ta ba shi bisa namijin kokari da ya yi a bangaren harkar man fetur da makamashin Gas a shekarar nan da muke ciki.

Maikanti Baru ya rugo ya dawo Najeriya domin dakile matsalar wuyan man fetur
Maikanti Baru

Kafin ya baro kasar Ingila, Dakta Baru, ya ce 'yan Najeriya su kwantar da hankalin su domin kamfanin mai na NNPC yana da wadataccen man fetur domin bukatar 'yan Najeriya.

Hakazalika hukumar ta NNPC ta bayyana, a jiya, cewar babu shirin karawa man fetur kudi sannan ta ce ta raba Tankoki makare da man fetur ya zuwa duk sassan kasar nan.

DUBA WANNAN: Majalisar Dattijai za ta gudanar da bincike a kan jami'an SARS bisa zargin cin zarafin jama'a

A sanarwar da hukumar ta fitar, ta ce farashin mai har yanzu yana a kan Naira 143/145 a kan duk lita guda, kuma ba zata kara ko sisi ba.

Hukumar ta NNPC ta kara jaddada aniyarta na aiki tare da kungiyoyi masu ruwa da tsaki a bangaren harkar man fetur domin domin ganin matsalar karancin man da ta fara kunno kai bata cigaba da yaduwa.

A karshe hukumar ta bukaci 'yan Najeriya da su yi watsi da duk wata jita-jita da farfaganda a kan batun karin kudin Mai.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng