Babban burina In ga na Zama Mai amfanawa alummata da kuma taimakon su – Dalibin da yayi zarra a ABU Zaria

Babban burina In ga na Zama Mai amfanawa alummata da kuma taimakon su – Dalibin da yayi zarra a ABU Zaria

Al-Ameen Bashir Bugaje gwarzon dalibin nan da ya yi zarra a bana, ya zarce Kowane dalibi da ya kammala shahararriyar jamiar Ahmadu Bello dake Zaria a shekarar nan ya bayyana babban burinsa a rayuwa.

A tattaunawar da dalibin yayi da shafin Rariya ya bayyana cewa jajircewar da yayi a harkar karatunsa ce ta kais a ga yin nasara.

Dalibin ya mika godiya ga Allah SWT, da ya ba shi wannan nasara, domin a cewar sa duk yadda ka ke so, sai yadda Allah ya so.

Ya kuma ce shiri burin sa a rayuwa shi ne ya gay a zamo mai amfanarwa ga alumma da kuma taimakon su.

Babban burina In ga na Zama Mai amfanawa alummata da kuma taimakon su – Dalibin da yayi zarra a ABU Zaria
Babban burina In ga na Zama Mai amfanawa alummata da kuma taimakon su – Dalibin da yayi zarra a ABU Zaria

Sannan ya mika godiyarsa ga shugaban kamfanin matatar mai ta kasa wato Mai Kanti Baru da ya dauki nauyin karo karatunsa a duk inda yake so a duniya, a cewarsa hakan zai bashi damar tarayya da wasu kwararru na duniya.

KU KARANTA KUMA: Gazawar gwamnati ne silar zub da jini a Najeriya – Sarkin Musulmi

Ya ce: "Da farko dai ina mika godiya ga Allah SWT, da ya ba ni wannan nasara, saboda duk yadda ka ke so, sai yadda ya so.

“Ina shawartan dalibai da su kara maida hankali a Wajen karatunsu. Su kuma Matasa ya Kamata su dage Wajen neman ilimi, rayuwar nan dole Sai da ilimi za Ka iya ba da gudummuwa ga Al'umma. Wajibi ne kowa ya tashi ya nemi ilimi nan.

“Na yi matukar farin cikin da yadda suka Kara man Kwarin gwiwa, yadda Zan hadu da Wasu Kwararru na duniya a kara bugawa. Haka kuma ina mika godiya ga shugabanta Mai Kanti Baru da wannan dama da ya bani kuma zan Kara jajircewa a can ma, a dawo gida a Ga yadda Zaa taimaki Al'umma.”

A baya Legit.ng ta rahoto cewa hukumar NNPC za ta dauki nauyin karatun Dalibin da ya kammala Digiri da maki 4.93 cikin 5.00 a Ahmadu Bello ta Zariya.

A cikin wadanda su ka gama da matakin da ya fi na kowa Al-Ameen Bugaje ne a sama wanda yayi Digiri a ilmin zama Injiniyan wuta. Shugaban Hukumar NNPC Dr. Maikanti Baru yace Kamfannin NNPC za ta biya masa kudin karatun Digiri na 2 da 3.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng