Ranar bikin ala'adun kabilar Igbo: Gwamna Bagudu ya bawa al'ummar Igbo dake Kebbi gudunmawar Naira miliyan 10
- Kabilar Igbo na bikin ranar ala'adun gargajiya
- Gwamnatin Jihar Kebbi ta basu gudunmawar miliyan 10
- Anyi kira ga kabilun Najeriya da su zauna lafiya da juna
Gwamnatin jihar Kebbi ta ce ta bayar da gudunmawar Naira miliyan 10 ga al'umma kabilar Igbo dake jihar domin nuna murnar ta ga bikin tunawa da ranar al'adu ta 'yan kabilar Igbo.

Da yake bayyana bayar da gudunmawar ga 'yan kabilar ta Igbo, sakataren yada labaran gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Muazu, ya ce gudunmawar tamkar albishir ne ga 'yan kabilar Igbo cewar Jihar Kebbi gida ce wurin su.
Gudunmawar na zuwa ne daidai lokacin da 'yan kabilar Igbo ke bikin tunawa da ranar al'adun su a jihar.
Gwamna Bagudu ya ce suna taya 'yan kabilar Igbo murnar wannan biki tare da kira ga jama'a da su zauna lafiya da juna.
DUBA WANNAN: Ta tabbata: Atiku ya bayyana komawar sa jam'iyyar PDP
Hakazalika ya tabbatarwa da 'yan kabilar Igbo mazauna jihar cewar su cigaba da harkokin su cikin kwanciyar hankali domin su ma 'yan kasa ne kamar kowa.
Da yake jawabi, shugaban kabilar Igbo mazauna jihar, Cif Samuel Nnamani, ya yabawa gwamnan bisa wannan gudunmawa da ya basu tare da bayar da tabbacin cewar 'yan kabilar Igbo zasu cigaba da zama lafiya da mutanen jihar.
Nmani ya ce kabilar Igbo na goyon bayan zaman kabilu daban-daban a matsayin kasa daya.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng