Hukumar JAMB ta sanar da ranar da za ta fara sayar da fom din jarabawa
- Hukumar JAMB za ta fara sayar da fom din jarabawa ranar 6 ga watan Fabrairu na shekara 2018
- JAMB za ta sayar da fom din jarabawa a farashin naira N5,000 kuma za a biya naira N500 na sayan takarda sharrudan yin rijista
Hukumar gundanar da jarabwar shiga jami’a na kasa (JAMB) ta sanar da ranar da zata fara sayar da form din jarabawar 2018.
Hukumar ta ce za ta fara sayar da fom a ranar 6 ga watan Fabrairu na shekara 2018.
Mai magana da yawun hukumar, Fabian Benjamin, ya bayyana haka ne a zantawar da yayi da yan jaridar PREMIUM TIMES a ranar Lahadi.
Yace za a sayar da fom din a farashin naira N5,000 kuma za a biya naira N500 na sayan takardar sharrudan yin rijista.
KU KARANTA : Shekara 8 da barin mulki an mayar da gidauniyyar Turai Yar’Adua na kula da masu ciwon daji zuwa gonar wake
Hukumar ta shawarci duk dalibin da yake son ya rubuta jarabawar gwaji na (JAMB MOCK) yayi kokari yin rijista kafin ranar 31 ga watan Disamba.
Za a rubuta jarabawar a ranar Laraba 22 ga watan Janairu na shekara 2018, dalibai za su biya N700 kudin rijistar jarabawar gwaji na Mock.
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng