Yola: Har yanzu ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin garin Numan
- Har yanzu ana ci gaba da zaman dar-dar a yankin garin Numan, sakamakon kisan gillar da aka yi wa wasu Fulani
- Jama'a da dama suna yin hijira da iyalan su zuwa makwabtan jihohi saboda yiwuwar barkewar sabuwar rikici a yankin
- Rahotanni sun tabbatar cewa an sake aika wasu karin jami'an tsaro daga hedkwatar 'ƴan sandan de ke Yola
Tun harin ta'addancin da ake zargin 'ƴan kabilar Ɓachama, suka ƙaddamar akan wasu fulani a garin Numan da ke jihar Adamawa a makon jiya, ana ci gaba da zaman zullumi, sakamakon fargabar yiwuwar barkewar sabuwar rikici a yankin.
Yanzu ana jita-jitar cewa Fulani na shirin ɗaukar fansa, wanda hakan ya sa jama'a da dama suna yin hijira da iyalan su zuwa makwabtan jihohi.
A wata zantawa da majiyar Legit.ng, wani mazaunin garin Numan ya shaida ta wayar tarho cewa "Tunda aka tura jami'an 'yan sanda na Mopol domin kwantar da tarzoma da ta barke a kauyukan da rikicin yafi kamari, sai ɗazu muke ganin an wuce da gawarwakin wasu jami'an 'yan Sanda, daga nan ne jama'a suke tururuwar barin gari."
Rahotanni daga yankin sun tabbatar cewa hukumar 'yan sanda daga babbar hedkwatar ta de ke Yola, babban birnin jihar ta sake aika karin jami'an tsaro.
KU KARANTA: Hukumar 'yan sanda ta mayar da martani bisa korafin 'yan Najeriya a kan jami'an SARS
Kawo lokacin da aka haɗa wannan rahoto babu wani karin bayanai da aka fitar daga hukumar ta 'ƴan sanda.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng