Ba za mu yarda a saba wa Allah a otel dinmu ba – Kungiyar Izala
- Shugaban kungiyar Izala Abdullahi Bala Lau ya ce bukata ce yasa suka gina masaukin baki a Abuja
- Malam Bala Lau ya ce a matsayin su na kungiyar Addini baza su bari a sabawa Allah a Otel din da su gina ba
Shugaban kungiyar Izala na kasa Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya ce bukata ce ta sa kungiyar ta gina katafaren Otel a Abuja.
Malamin ya ce sun gina Otel din ne dan samar wa mallaman su masauki a birnin Abuja.
Abdullahi Bala Lau yace, yakamata a matsayin na mallamai addini su samu kebabben wajen saukar da baki da aka tsara shi bisa ka’idojin addinin Musulunci.
Kuma a matsayin su na kungiyar Addini ba za su bari ana sabawa Allah a ciki wajen masaukin bakin da suka gina ba.
KU KARANTA : Gwaman jihar Borno ya ce ba zai nemi kowani matsayi ba a zaben 2019
Malamin ya bayyana hakane a hirar da yayi da BBC hausa a birnin Landan a makon da yagabata.
A cikin watan Agusta na shekara 2017 kungiyar Izala ta bude sabuwar katafren otel din da ta gina a birnin Tarayya Abuja a unguwar Life Camp.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng