Yawaitar jini a jiki yana kawo cikas ga lafiyar dan Adam - Bincike
Kwararrun masana kiwon lafiya na birnin Benin dake jihar Edo, sun yi gargadi a ranar da ta gabata cewa, yawan jini a jikin dan Adam illa ne ga lafiyar sa.
Saboda haka masana kiwon lafiyar suke gargadin'yan Najeriya musamman masu yalwar jini a jikin su da su rinka bayar da tallafin jinin su duk bayan watanni shida domin ceton rayukan mutane masu bukatar jini.
Legit.ng ta fahimci cewa, masana kiwon lafiyar sun bayyana hakan ne a yayin gudanar da wani shiri na bayar da jini kyauta a babban asibitin Benin wanda wanda gwamnatin jihar Edo ta dauki nauyin shirya wa tare da hadin gwiwar kungiyar kiwon lafiya ta mata da kuma gidauniyar Tom Obaseki.
KARANTA KUMA: Wasu kungiyoyin jami'o'i zasu sake shiga yajin aiki gadan-gadan
Rahotanni sun bayyana cewa, kwamishinan lafiya na jihar Edo, Dakta David Osifo yake kira ga 'yan najeriya akan sun rinka bayar da tallafin jinin su domin babban matsalar da yake fuskanta a matsayin sa na likitan yara shine malalar jini a yayin tiyata.
LATSA WANNAN: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng