Kasar Israila na koyawa sojin samar Najeriya yada ake yakin sunkuru da masu ta'adda
- Kasar Yahudun Israila, wadda ta dade tana yaki da makwabta da ma masu sunkuru irin na 'yan ta'adda, ta ddauki aniyar koyarda sojin Najeriya yada ake yi
- A yanzu dai sojin Najeriya sun gagara murkushe Boko Haram a watanni 6 kamar yadda suka yi alwashi a baya
- Sauran kadan a gama da burbushin mayakan, amma har yanzu ba'a sami ceto matan chibok ba
A halin da arewar Najeriya ke ciki a yakin da ake gwabzawa dda Boko Haram, an sami wasu lokutan da kamar a mulkin PDP, mayakan kan iya kwace kauyuka su kuma tafi da mata da yara daji.
A yanzu Israila ta aiko agajin masu koyar da sabbin dabaru na yakin sunkuru da ma iyar da kakkabe sauran mayakan Boko Haram.
DUBA WANNAN: Atiku ya ce kasuwancin shekaru 40 ya tara masa dukiya ba kwarapshin ba
Sabbin matakan, sun hada da dambe, kwace makami hannun mayaki, ceto mata da yawa, da ma jewa zuwa shelikwapta domin barin filin daga.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng