Kada ku hana sana'ar kabu-kabu - Ameachi ya roki Jihohi
- Ministan sufuri, Rotimi Ameachi ya shawarci Jihohi su kyale al'umma su cigaba da amfani da babura don yin kabu-kabu domin suna saukaka rayuwar al'umma
- Ministan yayi wannan rokon ne a wajen taron kaddamar da sakatariyar hadadiyar kungiyar masu kabu-kabu, gyran babura da babura masu kafa uku
- Daga karshe ya shawarci masu kabu-kabun su bi doka da oda wajen ayyukansu kuma su cigaba da karo ilimi domin kwarewa kan aikin su
Ministan sufuri Rotimi Ameachi yayi kira ga Johohi da kananan hukumomi a Najeriya su dena hana yin kabu-kabu da babur da kuma babur mai kafa uku, madadin hakan ya kamata su rungume su ne a matsayin hanyoyin sufuri.
Ministan yayi wannan maganar ne ranar Alhamis a garin Abeokuta, babban birnin Jihar Ogun inda ya samu wakilcin mataimakiyar direkta a hukumar sufuri, Foluke Oni, wajen taron kaddamar da sakatariyar hadadiyar kungiyar masu kabu-kabu, gyaran babur da kuma babur mai kafa uku.
DUBA WANNAN: Hotuna: Dubi abinda Al-Makura ya aikata yayinda ya ga wani mutum dauke da yara 5 a babur
Ministan yayi amana da irin rawar da baburan suke takawa wajen saukake rayuwar al'umma da samar da aikin yi, ya kara da cewa a wasu kasashen duniya ma baburan ne abin da al'umma suke amfani dashi wajen zirga-zirga.
Amma duk da haka, yayi kira da masu amfani da baburan su rika amfani da hulunan kwano domin kare kansu daga buguwa idan hadari ya faru.
Ya kuma sharce su da kada suyi kasa a gwiwa wajen samun horo na tuki da kuma samar da insura ga ababen hawan nasu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng