Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya taya Wizkid da Davido murnar nasarar lashe lambar yabon MOBO da suka yi

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari ya taya Wizkid da Davido murnar nasarar lashe lambar yabon MOBO da suka yi

- Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Davido da Wizkid Murna kan nasara da suka samu na lambobin yabon MOBO

- Wizkid ya karbi lambar yabo a matsayin mawaki mafi nagarta na kasa da kawa yayinda Davido ya lashe lambar yabon mawaki mafi nagarta a Afrika

- Shugaban yace kasar tayi matukar murna da nasarori da suka samu

Legit.ng ta rahoto a baya cewa shahararrun mawakan nan masu suna Wizkid da Davido sun lashe lambar yabo a taro da aka shirya na wakokin bakaken fata wato MOBO.

Wizkid ya karbi lambar yabo a matsayin mawaki mafi nagarta na kasa da kasa bayan yayi nasara kan Drake, SZA, CardiB, JAY-Z, Kendrick Lamar yayinda Davido ya lashe lambar yabon mawaki mafi nagarta a Afrika bayan yayi nasara kan Eugy, Juls, Maleek Berry, Mr Eazi, Sarkodie da sauransu.

Yanzu, shugaba Buhari ya fito don taya mawakan biyu murna kan yanda suke daukaka kasar.

Ya aika musu sakonni ne a shafin zumuntansa na twitter.

KU KARANTA KUMA: An gano kayataccen hotunan Zahra Buhari-Indimi a wajen wani biki a Abuja

Haka zalika mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya taya mawakan biyu murna inda yake cewa duniya ta yaba wa kwazonsu d a iya aiki.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng