Wiz-Kid da Davido sun yi zarra a fagen waka na Duniya
– Mawakan Najeriya dai na cigaba da yin fice a Duniya
– Wiz Kid ya buge su Jay Z wajen wata kyauta kwanaki
– Haka Mawaki Davido ya zama Gwarzon MOBO na bana
Mun samu labari cewa a makon nan ne Mawakan Najeriya Wiz-Kid da Davido sun yi zarra a fagen waka na Duniya inda su ka sha gaban sauran Mawakan Kasar waje wajen wasu kyauta.
Davido da Wiz-Kid wadanda ake ji da su a Najeriya sun kece raini a wajen bada lambar yabo na MOBO da aka yi a Birnin Leeds na Kasar Ingila. Har dai Shugaban Kasa Buhari da Mataimakin sa Yemi Osinbajo sun taya Mawakan Kasar murna.
KU KARANTA: Fati Abubakar ta bayyana fim din da ya fi ba ta wahala
Wiz-Kid ya doke Mawakan Kasar waje irin su Jay-Z da Cardi B da kuma su Kendrick Lamar inda ya zama Tauraron Kasar ketare. Davido kuma ya buge Mawakan Duniya irin su Mr. Eazi da shi kan shi Wiz Kid ya zama Gwarzon Afrika na bana.
Kamar yadda labari ya zo mana dai sauran Mawakan Najeriya irin su Tiwa Savage da Tekno da Wande Coal ba su lashe kyautar komai ba a wajen bada lambar yabon na MOBO.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng