Malaman ƙungiyar Izala zasu gudanar da wa’azi a birnin Basalona na ƙasar Sifen
A cigaba da yawoce yawocen Da’awah a kasashen Nahiyar Turai, malaman kungiyar Izalatil Bidi’ah Wa’iqamatissunnah, da aka fi sani da suna Izala sun wuce kasar Sifen da nufin wa’azi.
Wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Ibrahim Bello, ya bayyana haka a shafinsa na Facebook, inda ya daura hoton takardar tallar wa’azin.
KU KARANTA: Ana tare: Naji daɗin wani kyakkyawan albishir da Tinubu yayi min – Buhari
Majiyar Legit.ng ya ruwaito Malaman zasu gudanar da wa’azin farko a ranar 5 ga watan Disamba a garin Andalusia, yayin da zasu gudanar da wa’azin ranar 6 ga watan Disamnba a garin Basalona.
Daga cikin malaman da zasu yi wa’azi a ranar akwai shugaban kungiya, Sheikh Bala Lau, sakataren kungiya, Sheikh Kabiru Gombe da Sheikh Saifuddeen Abubakar.
Da fari dai tawagar Malaman ta fara yada zango a kasar Ingila ne, inda ta gabatar da wa’azi a garin Tottenham, inda suka yi karatu a kan ‘Aure a Musulunci’. Daga nan sai suka wuce kasar Greece.
Bayan nan kuma sai kasar Jamus, inda suka gabatar da wa’azi a a Masallacin Rahma dake garin Hamburg.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng