'Yan sanda da jami'an NSCDC zasu saka kafar wando daya da masu kaciyar mata

'Yan sanda da jami'an NSCDC zasu saka kafar wando daya da masu kaciyar mata

- Rundunar yan sanda da na NSCDC sunce zasu bazama wajen taka birki ga masu yima mata kachiya a yankin Kudu mas Yamma

- Shugabanin hukumomin sunyi wannan alkawarin ne a yayin da ake gudanar da wani taro na wayar da al'umma kan illar yima matan kachiya da wasu kungiyoyin kare hakkin bil adama suka shirya

- Shugabanin hukumomin tsaron sunce baza su raga ma masu aikata kachiyar tunda akwai dokar gwamnatin tarayya da tayi hani ga yin kachiyar ga mata

Rundunar yan sanda da hukumar NSCDC sunce baza suyi kasa a gwiwa ba har suj sun gano masu yima mata kaciya a Johohin Oyo, Osun da kuma Ekiti domin su gurfanar dasu gaban kotu su fuskanci hukunci.

'Yan sanda da jami'an NSCDC zasu saka kafar wando daya da masu kaciyar mata
'Yan sanda da jami'an NSCDC zasu saka kafar wando daya da masu kaciyar mata

Kwamandan hukumar NSCDC na Jihar Oyo, Mista John Adewoye da takwaran sa na Jihar Osun, Mr Akinwade Aboluwoye da kuma mataimakin kwamishinan yan sanda reshen binciken masu aikata manyan laifuka na Jihar Ekiti, Mista Ayodeji Lawal ne suka fadi dauki wannan alkawarin.

DUBA WANNAN: Gwamna Abdulaziz Yari ya kasa biyan albashi, ya bige da bambadanci

Jami'an tsaron sunyi dauki wannan alakawarin ne a jawabin da sukayi a wani taro na kwanaki 2 da Kungiyar kare hakkin mata ta shirya tare da hadin gwiwar wata kungiyar kare hakin bil adama mai zaman kanta da aka gudanar a yankin Kudu maso yamma.

Jami'an tsaron sunce tunda akwai dokar gwamnatin tarayya da ta haramta yima matan kaciya, baza suyi wata-wata ba wajen tabbatar da cewa al'umma sun bi dokar sau da kafa.

Har ila yau, shirin ya samu tallafin asusun taimaka wa yara na duniya UNICEF.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164