Yadda ake tilasta wa namiji ya fito da matar aure

Yadda ake tilasta wa namiji ya fito da matar aure

- Falalu A Dorayi ya bayyana dalilin da yasa ya shirya fim din Auren Manga

- Fitaccen jarumin Kannywood Baba Falalu ya ce ya shirya fim din Auren Manga dan ba mutane dariya

- Dorayi ya ce ya rubuta fim din ne da marigayi Rabilu Musa dan Ibro a matsayin jagoran kafin Allah yayi masa rasuwa

Shaharren daraektan finafinan Kannywood Falalu A Dorayi ya ca ya hada fim din “ Auren Manga” ne saboda ya ba mutane dariya.

A tattaunawar da Baba Falalu yayi da Nasidi Adamu Yahaya , ya ce ya tsara fim din ne yadda zai sha bam-bam da sauran fina-finan barkwanci.

Yace ya rubuta fim din ne mai suna “ Auren Manga” shekaru biyar da suka gabata da marigayi Rabilu Musa dan Ibro a matsayin jagoran fim din, sai kuma Allah yi yi masa rasuwa.

Yadda ake tilasta wa namiji ya fito da matar aure
Yadda ake tilasta wa namiji ya fito da matar aure

Dan haka yasa yayi gyare-gyare a fim din ya zama jagoran fim din shi da kan shi.

KU KARANTA : Buhari ne ya sa ministan Shari’a ya tattauna da ni sannan ya tabbatar da dawo dani bakin aiki – Inji Maina

Fim yana koyar da yadda ake tilastawa namiji ya fito da matar aure, wanda hakan ya bambanta da yadda aka saba.

Baba Falalu yace ya kashe naira miliyan biyu N2m wajen shirya wannan fim din

A cikin wadanda suke cikin wannan wasa akwai Adam a Zango, Hadiza Gabon Suleman Yahaya Bosho da sauran su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng