Kashi 66 daga cikin dari na magunguna jinyar zazzabin cizon sauro Malaria jabu ne
- Kungiyar kula da kiwon lafiya ta ce sama da kashi 60 na magunganar maganin cizon sauro jabu ne
- Kungiyar WHO ta ce jabun magunguna ke sanadiyar mutuwar duban kananan yara dake dauke da ciwon malaria
- Kamfanonin da ke sarrafa wannan maguguna samu dala biliyan $30 a kowani shekaara
Kungiyar Kula da harkan kiwon lafiya na duniya WHO ta ce kashi 66 na magungunar jinyar zazzabin cizon sauro Malaria a kasashen dake taso wa jabu ne.
A wata sanarwa mai tada hankali da kingiyar kiwon lafiya na duniya WHO ta fitar a jiya Talata, ta ce daya daga cikin magunguna goma da ake sayar wa a wannan kasashe jabune.
Kuma wannan magani ke sanadiyar mutuwar kananan yara da dama a wannan kasashe.
A gwaje-gwajen da kungiyar WHO ta tsakanin shekara 2007 zuwa 2016, wanda ya kunhi magunguna 46,000 ya nuna cewa kasha 10 a cikin dari na magungunan jabu ne.
KU KARANTA : Buhari ne ya sa ministan Shari’a ya tattauna da ni sannan ya tabbatar da dawo dani bakin aiki – Inji Maina
Kasashen Afrika musamman Najeriya sune kan gaba wajen siya wannan magunguna.
Bincike ya nuna kamfanonin da ke sarrafa wannan magununguna suna samun kudin da yake kimanin dala biliyan $30 a kowani shekara.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng