Cinnaka ba ka san na gida ba! Wata shahararriyar Giwa ta kashe mai ita

Cinnaka ba ka san na gida ba! Wata shahararriyar Giwa ta kashe mai ita

- Wannan al'amari ya faru ne a Arewacin garin Chiang Mai na kasar Thailand

- Giwan ta shahara domin kuwa ta bayyana a fina-finai da tallace-tallace

- Wannan al'amari ya janyo cece-kuce game da yin wasanni da giwaye domin nishadantarwa

A ranar Litini ne, a kasar Thailand a Arewacin garin Chiang Mai, wata Giwa ta murkushe mai ita, mai suna Somsak Riengngen, har lahira. Giwan ta shahara don kuwa ta bayyana a fina-finai da tallace-tallace da dama.

Cinnaka ba ka san na gida ba! Wata shahararriyar Giwa ta kashe mai ita
Cinnaka ba ka san na gida ba! Wata shahararriyar Giwa ta kashe mai ita

Giwan mai shekaru 32, ta na da nauyin ton 5, ta samu damar kashe Somsak, mai shekaru 53, bayan ya kwance ta. A nan ne fa ta kai ma shi wawura, ta murkushe shi.

KU KARANTA: Fa'idoji guda 7 na zubar da hawaye ga dan adam

Daraktan Chiang Mai na wucen gadi, mai suna Wuthichai Muangman, shi ne ya tabbatarwa manema labarai faruwan hakan. Wuthichai ya bayyana Somsak a matsayin mutum wanda ya san kan giwaye da dabi'un su.

Kasar Thailand dai ba boyayye bane wurin nishadantar da mutane ta hanyar wasanni da giwaye. sai dai kuma faruwan wannan mummunan lamari ya janyo cece-kuce, wanda hakan na iya kawo cikas a sana'ar wasa da giwayen.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164