Zaben 2019: Yadda 'yan siyasa ke neman karar da kwayayen angulu wajen tsafi

Zaben 2019: Yadda 'yan siyasa ke neman karar da kwayayen angulu wajen tsafi

Masana ilimin tsuntsaye sun fara kokawa game da yadda jinsin tsuntsuwar nan ta angulu ke neman karewa a Najeriya sakamakon yadda 'yan siyasar kasar ke farautar kwayayen ta ruwa a jallo da nufin yin tsafe-tsafen samun nasarar zaben 2019 mai zuwa.

Wasu daga cikin masanan da suka yi fira da majiyar mu sun bayyana cewa tuni dai 'yan siyasar kasar suka soma shiga kauyuka suna neman kwayayen da yanzu haka suka yi matukar karanci a fadin kasar sannan kuma suka shawarci gwamnati da ta fito da wani tsari da zai kawo karshen hakan.

Zaben 2019: Yadda 'yan siyasa ke neman karar da kwayayen angulu wajen tsafi
Zaben 2019: Yadda 'yan siyasa ke neman karar da kwayayen angulu wajen tsafi

KU KARANTA: An tsinci gawar wani jigon APC a jihar Katsina

Legit.ng dai ta samu cewa yanzu haka dai kwan na angulu kan kai zunzurun kudi har zuwa Naira miliyan 1 saboda yadda yayi karanci duk domin yin tsafi da shi da nufin lashe zaben mai zuwa.

Shi ma dai wani na kasuwa dake fataucin tsuntsaye a garin Uyo ya bayyana cewa hakika irin farautar da ake yi wa kwan yanzu haka ya fara sa jinsin tsuntsun fara karewa a dazukan kasar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng