Yoyon Fitsari: Za ayi wa mata aiki kyauta a asibitocin gwamnati
- Za a fara yiwa matan dake dauke da cutar yoyon fitsari kyauta a Asibitin gwamnati inji ministar kiwon lafiya
- Gwamanti ta hada gwiwa da kungiyar da ke kula da masu cutar yoyon fitsari mai suna ‘Engender Health/Fistula Care Plus’ dan kawo karshen wannan cuta
Gwamnatin tarayya ta umarci asibitocin gwamnati ta rika yi wa matan da ke fama da cutar yoyon fitsari aiki kyauta.
Sanarwar ya fito daga ofishin ministar kiwon lafiya ferfesa Isaac Adewale a ranar Litinin.
Ferfesa Isaac Adewale ya kara da cewa gwamanti ta hada gwiwa da kungiyar da ke kula da masu cutar yoyon fitsari da mai suna ‘Engender Health/Fistula Care Plus’.
KU KARANTA : Ban taba ambaton Sheikh Dahiru Bauchi a wa'azina ba — Kabiru Gombe
Kungiyar ‘Engender Health/Fistula Care Plus’ ta dauki nauyin samar wa asibitocin gwamnatin Najeriya da kayan aikin da magungunan da suke bukata.
Bincike ya nuna matan Arewacin Najeriya sun fi na kowani yankin kasar kamuwa da wannan cuta, wanda aurar da yara mata masu kanana shekaru ke janyo wannan cuta.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng