An tona asirin Maza masu auren da ke neman ‘Yan mata
- Wata budurwa ta kwancewa wani mutumi zani a kasuwa
- Mutumin ya kasance yana neman ta duk da yana da aure
- Yanzu Mazan aure sun fiye neman mutane saboda kwadayi
Mun samu labari cewa an fara tona asirin maza masu auren da ke neman ‘Yan mata. Wasu mazan da matan su da ma yara amma sai su rika neman ‘Yan mata a waje.
Wata Baiwar Allah mai suna Whitney ta fallasa wani mutumi da ke da iyali amma yake neman ta. Wannan Budurwa ta fito da zantawar da su kayi da wannan babban mutum a yanar gizo kamar yadda hotuna su ka shigo hannun mu.
KU KARANTA: Odi Okojie ya bar PDP bayan an ba matar sa mukami
Wannan Budurwa ta bayyanawa wannan mutumi mai aure cewa ba ta da sha’awar wani zantawa da shi tun da ta tabbata yana da iyali. Whitney ta nemi ya shafa mata lafiya duk da ya nemi su hadu su gana a matsayin su na abokan juna a Legas.
Jama’a dai da dama sun yabawa wannan mata a shafukan zumunta don kuwa ba kowa bane ke iya yin abin tayi saboda kwadayi na abin Duniya. Whitney ta fadawa wannan mutum ya kyale ta ko ita da ire-iren ta sa samu mazan aure.
Odi Okojie ne ya tsaya takara a Jam’iyyar PDP a matsayin Mataimakin Gwamnan Jihar a 2016 inda APC ta lashe zaben. Okojie ya taba rike mukamin Kansila a Jihar. Yanzu haka dai Prince Okojie ya bar Jam’iyyar PDP.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng