Yola: Sultan ya yi gargadi akan kisan gillar da ake yi wa Fulani
- Sarkin Musulmi ya yi gargadi a kan kisan Fulani a Numan, jihar Adamawa
- Sultan ya ce hakuri da kuma shiru na Fulani a kan kisan ‘yan uwansu ba wai tsoro ba bane
- Abubakar ya ce har yanzu ba a manta da abin da ya faru da Fulani a Mambilla, jihar Taraba ba
Mai martaba Sarkin Sakkwato, Sa'ad Abubakar III, a ranar Lahadi 26 ga watan Nuwamba, ya yi Allah wadai akan kisan gillar da aka yi wa wasu Fulani da dama a Numan a jihar Adamawa.
Sarkin Musulmi ya yi gargadin cewa hakuri da kuma shiru na Fulani a kan kisan da aka yi wa ‘yan uwansu a Adamawa ba wai tsoro ba bane.
Sultan ya byyana hakan ne a Yola lokacin da yake jawabi a wani taron bude gidan radiyon Pulaaku FM, mallakar Lamido na Adamawa, Muhammadu Barkindo.
Kamar yadda Legit.ng ke da labari, sarkin wanda sarkin Kano, Muhammad Sanusi II, ya wakilta a taron ya yi kira ne ta hanyar bincike kan kisan da aka yi a cikin garuruwan Numan guda hudu a jihar Adamawa.
KU KARANTA: Wata mata ta shafe wata 9 tana haukan karya domin kare 'yar ta daga Boko Haram
"Ina amfani da wannan dama don nuna tausayi ga mutanen Adamawa, a kan lamarin da ya faru a Numan; da kuma kira ga jami'an tsaro, don bincikar lamarin da kuma hukunta wadanda suka aikata wannan barna", in ji shi.
"Har yanzu ba mu manta da abin da ya faru da Fulani a Mambilla, jihar Taraba ba, muna jiran bayanai daga jami'an tsaro".
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng