Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

- Shugaban kungiyar Izala ya bayyana dalilin da yasa suka ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari

- Sheik Bala ya ce sun fa dawa shugaban kasa halin da talakwan Najeriya suke ciki

- Shehin Mallamin ya ce harda ayoyin kur'ani suka karanta masa

Shugaban kungiyar Izala na addinin muslunci na kasa (JIBWIS) Sheikh Abdullahi Bala Lau, ya fadawa BBC dalilin da su na kai ziyara fadar shugaban kasa.

A farkon watan Nawumba ne wasu malaman addinin musulunci na Najeriya suka kai wa shugaba Muhammadu Buhari ziyara a fadar sa dake Abuja.

Sheikh Abdullahi Bala Lau yace sun ziyarci Buhari a fadar sa ne saboda ya kwashe lokaci mai tsawo bai gana da mallaman addinin muslunci ba, tun gabanin ya fara jinyar san a farko a birnin Landan.

Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau
Na fada wa Buhari halin da talakawa suke ciki – Sheikh Bala Lau

Ba mallaman addinin muslunci kadai suka ziyarci shugaan kasa ba, hadda mallaman addinin kiritsa.

KU KARANTA : An nada tsohon shugaban tsagerun Neja delta Ateke Tom sarkin garin Okorichi a jihar Rivas

Shugaban kungiyar Izala yace "babu shakka sun shaidawa ma shugaban kasa halin da al’ummar Najeriya suke ciki musamman talakawa.

"Hadda ayyoyin kur’ani sai da muka karanta masa” inji Bala Lau.

Kuma shugaban kasa ya ba su tabbacin cewa zai yi amfani da shawarwarin su

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng